Eid-el-Fitr: GARO YA BUKACI AL’UMMA DA SU DAUKI DABI’AR HAKURI TARE DA HADIN KAI DON WANZAR DA ZAMAN LAFIYA

IMG 20220502 WA0001
IMG 20220502 WA0001

Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC, Alhaji Murtala Sule Garo ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi koyi da darusan da suka koya a watan Ramadana tare da inganta hadin kai da zaman lafiya domin ci gaban jihar da ma kasa baki daya.

A cikin sakonsa na barka daa Sallah ga Musulmi, wanda ya aikewa jaridar Solacebase a ranar Lahadi, Garo ya jaddada bukatar hadin kai da hakuri don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu ya yi kira ga al’ummar musulmin jihar Kano da su yi amfani da wannan damar wajen yin tunani a kan ayyukan da suka yi a baya don gyara kuskurensu.

Ya kuma ce akwai bukatar al’umma su yi koyi da Manzon Allah (SAW), ta hanyar sadaukarwa a cikin hidimominsu na duniya, domin amfanar da marasa galihu a cikin al’umma.

Galadiman Garo ya bukaci jama’a a yayin bikin cewa kar su manta da halin karamci da kuma tallafawa marasa karfi a cikin al’umma.

“Ina amfani da wannan dama domin taya gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje murnar kammala azumin watan Ramadana da kuma shaida bikin Sallah,” in ji sakon.

“Hakazalika, ina taya Sarakunanmu na masarautu guda 5 murna da kuma al’ummar Kano nagari tare da goyon bayan gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje bisa yunkurin gina sabuwar Kano domin al’umma su amfana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here