Cikakkun jerin sunaye: Majalisar kula da ilimin shari’a ta amince da jami’o’i 114 don gudanar da shirye-shiryen shari’a a Najeriya

Council of Legal Education 656x430

Majalisar kula da ilimin shari’a ta fitar da jerin jami’o’i 114 da ta amince su rika gudanar da shirye-shiryen karatun lauya a Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin wata takarda da aka fitar a ranar Juma’a wadda sakatariyar majalisar kuma daraktar kula da harkokin gudanarwa, Aderonke Osho, ta sanya wa hannu.

Majalisar ta bayyana cewa jami’o’in da ke cikin wannan jerin su kadai ne aka ba izinin karbar dalibai a shirin digirin farko na Shari’a wato LL.B a kasar.

Ta yi gargadin cewa duk wata jami’a da ke gudanar da shirin karatun shari’a ba tare da amincewar majalisar ba za ta fuskanci hukunci.

Majalisar ta kuma bayyana cewa daliban da aka karba a shirye-shiryen karatun shari’a da ba su da amincewa ba za su samu damar shiga makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya ba.

Ta kara da cewa duk wata jami’a da ta karbi dalibai a shirin karatun shari’a ba tare da amincewar majalisar kula da ilimin shari’a ba na aiki ne sabanin dokokin da ke tsara ilimin lauya a Najeriya kuma za a dauki matakin hukunci a kanta.

Majalisar ta kara da cewa za ta ci gaba da sabunta jerin jami’o’in da aka amince da su daidai da aikinta na kula da tsarin ilimin shari’a a Najeriya.

Daga cikin jami’o’in da aka amince da su akwai jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna, jami’ar Bayero da ke Kano, jami’ar Lagos, jami’ar Ibadan, jami’ar Najeriya da ke Nsukka, jami’ar Jos, jami’ar Maiduguri, jami’ar Ilorin da kuma jami’ar Abuja.

Haka kuma akwai jami’ar Skyline da ke Kano, jami’ar Azman da ke Kano, jami’ar Maryam Abacha da ke Kano, da kuma jami’ar ‘yan sandan Najeriya da ke Wudil a jihar Kano.

Majalisar kula da ilimin shari’a ita ce hukuma ta doka da ke da alhakin horaswa da kuma tsara tsarin kwarewar masu neman zama lauyoyi a Najeriya.

An kafa majalisar ne karkashin dokar ilimin shari’a, kuma ita ce ke kula da makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya tare da tabbatar da cewa ana kiyaye ka’idojin ilimin lauya a fadin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here