Gwamnan Ebonyi Nwifuru ya dakatar da kwamishinoni biyu

Francis Nwifuru 750x430

Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya dakatar da Kwamishinan Ayyuka, Engr. Stanley Lebechi Mbam, da Kwamishinan Raya Ababen More Rayuwa, Engr. Ogbonnaya Obasi Abara.

An dakatar da su ne bisa zargin sakaci wajen gudanar da ayyukansu, kamar yadda wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Dr. Monday Uzor, ya fitar a ranar Asabar ta bayyana.

Sanarwar ta ce an umarce su da su miƙa duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu, ciki har da motocin aiki, ga Sakataren Gwamnatin Jihar nan take.

Wani ɓangare na sanarwar ya ce: “Gwamnan Jihar Ebonyi, Mai Girma Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru, ya amince da dakatar da Engr. Stanley Lebechi Mbam, Kwamishinan Ayyuka, da Engr. Ogbonnaya Obasi Abara, Kwamishinan Raya Ababen More Rayuwa na wani lokaci ba tare da ƙayyadadden wa’adi ba, bisa zargin sakaci wajen aiki.

An umarce su da su miƙa duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu, ciki har da motocin aiki, ga Sakataren Gwamnatin Jihar nan take.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here