Wike da ƙungiyoyin ƙwadago sun cimma yarjejeniyar dakatar da yakin aiki da tsakar dare

Wike NBA 750x430

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tare da ƙungiyoyin ƙwadago masu tsari, sun cimma yarjejeniya da tsakar dare wadda ta kai ga dakatar da yajin aikin da ake yi tare da umarnin komawa bakin aiki nan take ga ma’aikatan da abin ya shafa.

An cimma yarjejeniyar ne bayan fiye da sa’o’i uku ana tattaunawa har zuwa wayewar gari, inda aka kammala da misalin ƙarfe uku da mintuna hamsin na dare.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Babban Birnin Tarayya, Sanata Mohammed Bomoi, ne ya jagoranci tattaunawar, a gaban shugabannin Kungiyar Kwadago ta Ƙasa NLC da Kungiyar Ƙwadago ta TUC.

Bayan kammala taron, mukaddashin babban sakataren NLC, Benson Upah, tare da babban sakataren TUC, Nuhu Toro, sun bayyana cewa an cimma wasu muhimman matsaya da nufin dawo da zaman lafiya a harkar aiki.

Daga cikin matsayoyin da aka cimma akwai tabbacin cewa babu wani ma’aikaci da za a gallaza masa saboda halartar yajin aikin, janye dukkan shari’o’in da aka shigar a Kotun Ƙwadago ta Ƙasa, da kuma alkawarin Ministan Babban Birnin Tarayya na ci gaba da mutunta juna tare da ci gaba da tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago.

Haka kuma, Ministan ya tabbatar wa ƙungiyoyin ƙwadago cewa za a rika tattaunawa da su a kai a kai domin magance duk wata matsala da za ta taso nan gaba.

Sakamakon haka, an umurci ma’aikatan da ke ƙarƙashin Kwamitin Ayyukan Ƙungiyoyin Haɗin Gwiwa JUAC, da kuma dukkan rassa na NLC da TUC a Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya, da su koma bakin aiki nan take.

Rigimar ta samo asali ne daga matsalolin aiki da ba a warware ba a Hukumar Babban Birnin Tarayya, lamarin da ya sa NLC da TUC suka shiga yajin aiki tare da barazanar gudanar da gagarumin zanga-zanga, duk da gargadin rundunar ’yan sanda ta Babban Birnin Tarayya kan matsalar tsaro da kuma umarnin kotu da ya hana gudanar da irin wannan yajin aikin.

Yajin aikin ya kawo cikas ga harkoki a Babban Birnin Ƙasa na tsawon kwanaki da dama kafin sa hannun Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Babban Birnin Tarayya ya kai ga warware matsalar gaba ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here