Cikin gaggawa: Gwamna Yusuf ya gana da Tinubu yayin da yake shirin sauya sheƙa

WhatsApp Image 2026 01 19 at 17.13.47 750x430

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a ofishinsa da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa ganawar na gudana ne a daidai lokacin da ake ta hasashe kan shirin gwamnan na sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Wasu bayanai daga jaridar Daily Trust sun nuna cewa ganawar na iya kasancewa da alaƙa da tattaunawar da ake yi kan yiwuwar sauya sheƙar gwamnan, duk da cewa ba a bayyana cikakken dalilin ganawar a hukumance ba.

Rahotanni sun ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya isa fadar shugaban ƙasa ne da misalin ƙarfe 4:10 na yamma, sanye da farar babban riga da hula ja.

A ‘yan makonnin da suka gabata, ana ta rade-radin cewa gwamnan na shirin barin jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki a ƙasa.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa tattaunawar ta samu tangarda sakamakon rashin cimma matsaya kan batun ba gwamnan tikitin takara kai tsaye a zaɓen 2027, lamarin da ya haifar da sabani tsakanin magoya bayan gwamnan da na jagoransa na siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here