Jami’ar kula da Gidan gyaran hali ta Najeriya ta lashe kyautar girmamawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta 2025

WhatsApp Image 2025 10 08 at 19.00.05 750x430

Babbar jami’ar kula da gidan ajiya da gyaran hali CSC Olukemi Ibikunle, daga hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCoS), ta lashe lambar yabo ta Trailblazer Award ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta shekarar 2025, wadda ake bai wa mata masu aiki a fannin adalci da gyaran hali.

Wannan girmamawa ta fito daga Sashen Ayyukan zaman Lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDPO), kuma Mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ce ta mika mata takardar yabo a wani biki da aka gudanar a cibiyar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York a ranar Laraba.

A cikin wata sanarwa daga sashen hulɗa da jama’a na Hukumar kula da gidajen ajiya da Gyaran Hali ta Najeriya, an bayyana cewa wannan kyauta na girmamawa tana  zaƙulo mata kwararru da suka nuna hazaka, jagoranci, kirkira, da sadaukarwa wajen tabbatar da adalci da ingantaccen tsarin gyaran hali a duniya baki ɗaya.

An bayyana cewa CSC Ibikunle ta samu yabo ne saboda jajircewarta wajen kawo sauye-sauye a tsarin gidan yari, kula da fursunoni, da kare hakkin ɗan Adam a cikin wuraren da suke tsare.

Karin labari:ICPC za ta gurfanar da wani Ɗan jarida na Kano bisa zargin almundahana

Jami’ar ta fito ne daga cikin mutane biyar da aka zaɓa daga sassan duniya bayan wani tsari na tantancewa mai tsauri.

Daga cikin waɗanda aka zaɓa akwai wasu jami’an hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran Hali ta Najeriya, inda Ibikunle ta samu wannan yabo bisa aikinta tare da Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (MONUSCO), yayin da wata jami’a, Sarah Adole, ta samu girmamawa a aikin ta tare da hukumar MINUSCO.

A ƙarshe, Ibikunle ta fito a matsayin wadda ta lashe gaba ɗaya, inda ta sami yabo daga ƙasashe daban-daban saboda gudunmawar da take bayarwa wajen gyaran hali, sake tarbiyya, da ƙarfafa rawar mata a fannin aikin tsaro.

Shugaban hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta Najeriya, Sylvester Ndidi Nwakuche, ya taya ta murna, yana cewa wannan yabo shaida ce ta ƙwarewa, ƙwarewar aiki da kuma sahihancin jami’an hukumar a idon ƙasa da duniya.

Ya kuma ce wannan nasara tana nuna yadda cibiyoyin ƙasa da ƙasa ke ƙara amincewa da hukumar wajen bayar da gudunmawa ga zaman lafiya da ci gaban tsarin gyaran hali a duniya.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here