Gwamnatin tarayya ta buƙaci talakawa su yi Azumi da addu’o’i na kwanaki 3 don samu wadatar abinci

food market

Ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya, ta ayyana shirin yin Azumi da addu’o’i na kwanaki uku domin neman  ɗaukin Allah a fannin noma a Najeriya.

A cewar wata sanarwar ma’aikatar da SolaceBase ta samu mai ɗauke da kwanan watan 11 ga watan nan da muke ciki na Yuni mai ɗauke da sa hannun Daraktar kula da albarkatun a ma’aikatar Misis Adedayo Modupe O., ta ce daraktoci da mataimaka su na ma’aikatar da sauran manya na daga cikin wadanda za su halarci taron addu’o’in.

Modupe ta ce, taron addu’ar an yi shi ne da nufin yin roƙon ga Allah da kuma goyon bayan kokarin gwamnati na tabbatar da ingantaccen tsarin samar da abinci mai ɗorewa a fadin Najeriya.

WhatsApp Image 2025 06 14 at 9.32.39 AM

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here