‘Yan bindiga sun sake kai hari gari Zaria, inda suka sace mutane 5 a Kasuwar Da’a dake yankin Dutsen Abba.
Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan ‘yan bindiga sun kai wani hari akan titin Kaduna zuwa Zaria, inda suka kashe mutane 3 tare yin awon gaba da mutanen da ba a san adadin su ba.
Al’ummar yankin sun bayyana cewa da misalin karfe 1 na dare ‘yan bindiga suka shiga kauyen Dallatu inda suka sace mutane 2, daga bisani suka wuce kauyen kasuwae Da’a inda suka yi awon gaba da mutane 6, ciki harda kanan yara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a safiyar lau laraba ‘yab bindigar sun sako kanan yaran da suka yi garkuwa dasu.
Zuwa yanzu rundunar ‘Yan Sanda bata ce komai ba.













































