Kamfanin Coca-Cola zai tallafawa matasa 20,000 a Kano

BB2B0A02 0337 4BFF A3C8 976F236EED7D
BB2B0A02 0337 4BFF A3C8 976F236EED7D

Gidauniyar kamfanin Coca-Cola da hadin guyiwa da Gidauniyar Kamfanin Whitefield sun shirya domin tallafawa matasan jihar Kano kimanin dubu ashirin ta karkashin shirin bayar da tallafi mai taken “Equip Kano”.

Da take jawabi a wajen taron, Babban Daraktan Gidauniyar Whitefield  Fummi Johnson ta ce sun shirya tallafawa matasa sama dubu tamin da bakwai a duk fadin Nigeria, idan suka kudiri aniyar tallafawa matasa miliyan daya daga yanzu zuwa shekarar 2024.

Ta ce an kirkiro da shirin ne domin tallafawa matasa su zama masu dogaro da kan su.

Ta kara da cewa a wannan karon za’a tallafawa matasa dubu sittin, amma duba da muhimmancin da jihar Kano ke dashi aka warewa jihar kimanin mutane dubu ashirin.

A cewar Fummi Johnson yanzu haka fiye da mutane dubu goma sun yi rigistar shiga tsarin tallafin ta Intanet, inda ta bukaci sauran matasa da su dage wajen ganin sun amfana da shirin.

A nata jawabin Daraktan hulda da jama’a na kamfanin Coca-Cola Nwamaka Onyemelukwe, ya ce daga lokacin da aka kafa kamfanin zuwq yanzu kamfanin ya kashe fiye da dalar amurka billiyan biyu domin tallafawa al’umma a kasashe da dama.

Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano Kabiru Ado Lakwaya ya godewa Gidauniyar bisa bawa jihar Kano fifiko wajen zabar adadin fa ya fi na ko wace jihar, yana mai bayyana cewa hakan zai taimaka wajen bunkasar tallafin arzikin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here