A Gabatar Da Bincike Ga Fadar Shugaban Kasa Da Ministoci – Bello Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bukaci shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Malam Abdulrasheed Bawa da ya koma gefe, a gurfanar da shi gaban kuliya, a kuma binciki fadar shugaban kasa da mambobin majalisar zartarwa ta tarayya.

Matawalle, a cikin wata sanarwa, ya bukaci shugaban na EFCC da ya tabbatar da cewa binciken hukumar ya shafi kowa da kowa ba zaɓaɓɓu kadai ba, ta yadda ake cin zarafin gwamnoni kadai.

“Wannan ya ci karo da tanadin hukumar yaki da cin hanci da rashawa, wato idan da gaske Malam Bawa yake yi.

“Ina bukatar shugaban hukumar EFCC ya yi irin wannan bincike ga jami’an fadar shugaban kasa da ‘yan majalisar zartarwa ta tarayya, wadda ita ce mafi girman matakin gwamnati a kasar nan.

“Don samun, ya zama wajibi binciken cin hanci da rashawa, yabi taka shi kan sa Abdulrasheed Bawa domin gudanar da bincike akan sa, kamar yadda ni da wasu fitattun ‘yan Najeriya ke zargin sa da cin hanci da rashawa, karya doka da cin amanar jama’a da cin zarafin ofishinsa da hukumar da ke karkashinsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here