A halin yanzu mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya da ke gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da ministoci da dama da suka hada da na yada labarai da al’adu, Lai Mohammed; Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministocin kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Zainab Ahmed, na ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, da sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da na wutar lantarki, Abubakar Aliyu.
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Folashade Yemi-Esan da sauran Ministoci suna halartar taron ta yanar gizo daga ofisoshinsu da ke Abuja.
Osinbajo ya jagoranci zaman ne ba tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba da ke halartar babban taron bunkasa zuba jari karo na 5 a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
Akwai Karin bayani anjima………













































