Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa lamarin sace mutane da aka ruwaito a Kurmin Wali, wani yanki mai nisa a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, ya faru ƙwarai, duk da ruɗanin bayanai da suka haifar da tashin hankali a baya.
Rundunar ta fayyace cewa martanin farko da ta bayar ba musanta faruwar lamarin ba ne, sai dai matakin taka tsantsan yayin da ake tantance cikakkun bayanai daga jami’an da ke filin aiki domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.
Tun farko, rahoton ya bayyana lamarin a matsayin hari da aka kai wa masu ibada a coci, inda shugabannin coci da ƙungiyoyin farar hula suka nuna cewa an sace fiye da mutane 160 yayin ibadar Lahadi, ciki har da waɗanda ke cocin Cherubim da Seraphim a yankin.
Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa bayan samun rahoton, gwamnan jihar Kaduna ya kira taron majalisar tsaron jihar a gidan gwamnati, inda wasu daga cikin mutanen yankin da abin ya shafa suka yi jayayya kan sahihancin rahoton, lamarin da ya haifar da buƙatar ƙarin tantancewa kafin fitar da cikakken bayani ga jama’a.
Bayan kammala bincike daga sassan aiki da na bayanan sirri, rundunar ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru, tare da kaddamar da ayyukan tsaro na haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin gano inda aka kai mutanen da aka sace da kuma ceto su cikin aminci.
Sufeto Janar na rundunar ƴan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin tura muhimman dakarun aiki da na leƙen asiri zuwa Kajuru da yankunan da ke kewaye, ciki har da rundunonin dabara, ƙarfafa sintiri, ayyukan bincike da ceto, da matakan kare rayuka da dukiyoyi.
Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta bukaci jama’a da kafafen yaɗa labarai su yi haƙuri tare da dogaro da bayanan hukuma da ake fitarwa, tare da gujewa yada jita-jita ko labaran da za su iya kawo cikas ga ayyukan tsaro ko ƙara tayar da hankalin al’umma.












































