Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari ga al’ummar Doma da ke ƙarƙashin gundumar Tafoki a ƙaramar hukumar Faskari ta Jihar Katsina, inda suka kashe kimanin mutane 20 a tsakar rana ranar Talata.
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa ‘yan bindigar sun mamaye yankin ne da rana, suka ci gaba da aikata ta’addanci har zuwa misalin ƙarfe huɗu na yamma kafin su janye.
Shaidun gani da ido da suka nemi a sakaya sunansu sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma ƙone gidaje da dama a yankin yayin harin.
Harin ya faru ne duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a baya tsakanin ‘yan bindigar da al’ummar yankin.
Shugaban yankin, Alhaji Surajo Aliyu-Daudawa, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana shi a matsayin harin ramuwar gayya, yana mai cewa shi ne mafi muni cikin watanni biyar da suka gabata.
Aliyu-Daudawa ya ƙara da cewa an kwashe gawarwakin waɗanda aka kashe, kuma za a yi musu jana’iza a garin Tafoki da safiyar Laraba, inda ya jajanta wa al’ummar yankin tare da addu’ar Allah ya kiyaye aukuwar irin wannan hari a nan gaba.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa mutane 13 ne suka mutu a harin, kamar yadda kakakin rundunar DSP Aliyu Abubakar ya sanar a ranar Talata.
A cewar sa, bayan samun kiran gaggawa, jami’an ‘yan sanda tare da sojoji da ‘yan sintirin tsaron al’umma na Jihar Katsina sun garzaya wurin, amma maharan sun tsere kafin isowarsu.
NAN













































