Ƴan bindiga sun kashe jami’an NSCDC 8, sun sace ɗan kasar China

Gunmen scaled 1 750x430 (1)

Ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun hallaka jami’an tsaro na NSCDC guda takwas a wani hari da suka kai a kamfanin BUA Cement da ke Okpella, Jihar Edo, da daddare a ranar Juma’a.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe goma na dare, lokacin da jami’an NSCDC ke rakiya ga wasu ’yan kasar Sin guda biyar bayan kammala sintiri.

A cewar wata majiya, ’yan bindigar sun bude wuta a kan jerin motocin jami’an, inda aka kashe jami’an NSCDC takwas da kuma wani ɗan gari. Duk da haka, an samu nasarar ceto ’yan kasar Sin hudu, yayin da ɗaya daga cikinsu aka yi awon gaba da shi.

Karin karatu: Kaduna: ‘Yan sanda sun gayyaci El-Rufai, da wasu shugabannin jam’iyyar ADC

Harin ya kuma jikkata wasu jami’an NSCDC guda huɗu, wadanda yanzu haka suna jinya a asibiti da ba a bayyana ba.

Bayan faruwar lamarin, kwamandan NSCDC na Jihar Edo, Gbenga Agun, ya ziyarci wurin da abin ya faru tare da duba lafiyar wadanda suka jikkata.

Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na NSCDC a jihar, Efosa Ogbebor, ya ce ba zai yi tsokaci ba a yanzu, domin za a fitar da sanarwa daga hedikwatar NSCDC ta kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here