Ƙungiyar ƙwallon ƙafar mata Super Falcons ta samu tikitin zuwa gasar WAFCON ta 2026 a Morocco

Super Falcon new 750x430

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasa Super Falcons, ta samu Tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata (WAFCON) da za a gudanar a ƙasar Morocco a shekara ta 2026.

A ranar Talata ne Super Falcons suka tashi 1 da 1 da ƴan wasan ƙasar Benin a wasan dawowa na neman gurbin shiga gasar, wanda aka buga a filin wasa na MKO Abiola dake Abeokuta.

Ƴar wasan bay, Ashleigh Plumptre, ce ta fara cin ƙwallo a minti na 11 ta hanyar bugun kusurwa, wanda ya ƙara wa ƴan wasan Benin ƙunci tun bayan rashin nasara da suka yi a wasa na farko da ci 2 da babu a Lome.

A karawa ta biyu ne ƴan wasan Benin suka nuna ƙarfin guiwa, inda Yasminath Djibril ta zura ƙwallo kai tsaye daga bugun kyauta a minti na 61, ta doke mai tsaron ragar Najeriya, Chiamaka Nnadozie.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa ƴan wasa Deborah Abiodun da Esther Okoronkwo sun samu rauni a wasan, lamarin da ya sa aka maye gurbinsu.

Kocin Super Falcons, Justine Madugu, ya bayyana cewa duk da wasan bai kai yadda ake so ba, yana farin ciki da samun gurbin shiga gasar.

Ƴan wasan Super Falcons, masu lashe kofin Afirka sau goma, za su yi ƙoƙarin lashe karo na goma sha ɗaya a gasar WAFCON ta 2026 da za a gudanar a ƙasar Morocco.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here