Yan ta’addar Lakurawa sun kashe ‘yan banga 13 a Kebbi

gunmen new 1

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’addar Lakurawa ne sun kai hari kauyen Morai da ke karamar hukumar Augie a jihar Kebbi, inda suka kashe ‘yan banga akalla 13.

Wani shaidar gani da ido mai suna Alhaji Augie ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bangan sun yi garkuwa da su ne a wasu ciyayi da ke kusa da wurin bayan sun samu bayanan wani harin da ake shirin kai wa.

A cewarsa, maharan sun isa wajen inda suka yi yunkurin yin awon gaba da garken shanu.

Daga nan ne ‘yan banga suka kaddamar da wani kwanton bauna a yunkurin kwato shanun tare da fatattakar maharan.

Karin karatu: Mutane 40 sun rasu tare da lalata gidaje 383 a harin da aka kai jihar Filato

Ya zuwa yanzu dai an gano gawarwaki shida tare da yi musu jana’izar, yayin da ake ci gaba da neman sauran gawarwakin.

Sai dai duk kokarin samun amsa daga rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ya ci tura, domin mai magana da yawun rundunar, Nafiu Abubakar, bai amsa kiran waya ko sakon kar ta kwana da aka aika a layinsa ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here