WCQ: Najeriya ta doke Gabon da ci 4-1 a wasan neman cancantar buga wasan cin kofin duniya ta 2026

Super Eagles sabo 750x430

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles ta samu nasara mai ban sha’awa bayan ta doke ƙasar Gabon da ci 4-1 a ƙarin lokaci, wanda ya bai wa Najeriya damar zuwa zagaye na ƙarshe na wasan share fage a gasar cin kofin duniya ta Afirka ta 2026, a filin wasa na Stade Mohammed V dake Rabat, ƙasar Maroko.

Bayan mintuna 45 na farkon wasa ba tare da ci ba, Akor Adams ne ya fara zura ƙwallo ta farko a ragar Gabon a farkon rabin lokaci na biyu, bayan wata kura da ɗan wasan Gabon ya yi.

Sai dai ƙungiyar Gabon ta farke wasa mintuna huɗu kafin a tashi daga wasan, abin da ya tilasta a tafi ƙarin lokaci.

A ƙarin lokacin, Chidera Ejuke ne ya mayar da Najeriya gaba bayan wata kyakkyawar bugun ƙwallo, sannan Victor Osimhen ya ƙara ƙwallaye biyu don tabbatar da nasarar Super Eagles ɗin.

Tsaron baya na Najeriya karkashin jagorancin Benjamin Frederick da Calvin Bassey ya tabbatar da cewa ƙoƙarin Gabon na samun ƙarin kwallo bai yi nasara ba.

Wannan nasara ta kusantar da Najeriya shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026, yayin da wasan share fage na ƙarshe zai tantance matsayin ƙasar a hukuma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here