Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi kira ga ƙungiyar editoci ta ƙasa da su ci gaba da riƙe nagartaccen aiki na jarida cikin gaskiya da alhakin da ya dace, domin ƙarfafa Dimokuraɗiyya da haɗin kai a ƙasar nan.
Tinubu ya bayyana haka ne a wajen taron shekara-shekara na ƙungiyar editoci ta ƙasa da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya yaba wa ƙungiyar bisa yadda take ci gaba da gudanar da taruka masu tunani da nazari, yana mai cewa kafafen yaɗa labarai suna da muhimmanci wajen kare Dimokuraɗiyya da zaman lafiya.
Shugaban ƙasar ya ce taken taron, “Gudanar da Dimokuraɗiyya da Haɗin Kai: Rawar Editoci,” ya dace da lokacin da ƙasar ke ciki, inda ya jaddada cewa ya zama wajibi ga ‘yan jarida su riƙa gina amincewa da jama’a da kuma ƙarfafa alhakin ɗan ƙasa.
Ya tunatar da ‘yan jarida cewa kafafen yaɗa labarai sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasa, inda ya ce jaridun ƙasar Najeriya sun daɗe suna tsayawa wajen kare gaskiya da Dimokuraɗiyya har ma a lokacin mulkin kama-karya.
Tinubu ya gargadi masu aikin jarida game da barazanar yaɗa bayanan ƙarya musamman a wannan zamani na kafofin sada zumunta, inda ya nemi su riƙa tabbatar da gaskiya da daidaito a duk wani rahoto da za su wallafa.
Ya kuma ce, manufar aikin jarida ita ce ta taimaka wajen gina ƙasa, ba rushe ta ba.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin sa na ci gaba da ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro, bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ci gaban da ya haɗa kowa, ta hanyar sauye-sauyen da ke ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar.
A cewar sa, gina ƙasa yana buƙatar haɗin kai da fahimtar juna tsakanin gwamnati da kafafen yaɗa labarai.
A nasa jawabin, ministan yaɗa labarai da daidaita ra’ayoyi, Mohammed Idris, ya bayyana wannan taro a matsayin tarihi domin kuwa shi ne karo na farko da wani shugaban ƙasa mai ci ya halarci taron ƙungiyar editoci.
Ya yabawa Tinubu bisa jajircewarsa wajen kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai da kuma Dimokuraɗiyya.
Idris ya ce gwamnatin yanzu ta samar da yanayi mai kyau ga kafafen yaɗa labarai, inda fiye da tashoshi dubu ɗaya ke aiki ba tare da wata tsangwama ko rufe su ba saboda bayyana ra’ayinta.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin kafafen yaɗa labarai, tsoffin editoci da sauran manyan ‘yan jarida daga sassan ƙasar.
Daga cikin manyan baki da suka halarta akwai gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da tsohon gwamnan Ogun, Olusegun Osoba.
Taken ƙaramin taron da aka haɗa da babban taron shi ne, “Gaskiya a Zaɓe da Rashin Amana: Abin da ‘Yan Najeriya ke Sauraro a Shekarar 2027.”












































