Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban hukumar NDLEA ta ƙasa

WhatsApp Image 2024 09 05 at 14.51.14 750x430

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsawaita wa’adin naɗin Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa mai ritaya a matsayin shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an fara nada Marwa wannan kujera ne a watan Janairun shekarar 2021 a lokacin shugabancin Muhammadu Buhari, bayan ya jagoranci kwamitin shawara na shugaban kasa kan kawar da amfani da kwayoyi tsakanin shekarar 2018 zuwa Disamba 2020.

Wata sanarwa daga mai bai wa shugaban kasa shawara kan bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ta bayyana cewa tsawaita wa’adin zai bai wa Marwa damar ci gaba da jagorancin hukumar har zuwa shekarar 2031.

Marwa ya taba gwamnan soji a jihohin Legas da Borno, kuma ya yi karatu a makarantar soji ta Najeriya da kwalejin tsaro ta kasa.

Ya yi aiki a matsayin babban jami’in rundunar ta 23 mai dauke da makamai, mataimaki na kusa ga shugaban hafsoshin sojoji, da kuma rajistaran kwalejin tsaro ta kasa, baya ga ayyukansa a ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Washington da kuma ofishin wakilan Najeriya a majalisar dinkin duniya.

Ya mallaki digiri na biyu har karo biyu, a fannoni da suka shafi gudanarwa da hulda tsakanin kasa da kasa daga jami’ar Pittsburgh da jami’ar Harvard.

A lokacin jagorancinsa a hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, an samu nasarorin kama mutane fiye da dubu saba’in da uku da ke da hannu a sha ko fataucin kwayoyi tare da kwace tan miliyan goma sha biyar na kwayoyi iri-iri.

Hukumar ta gudanar da gangamin faɗarwa a fadin kasar nan domin dakile amfani da kwayoyi, lamarin da ya kara karfafa yaki da matsalar.

Tsawaita wa’adin Marwa ya nuna amincewa da irin rawar da yake takawa wajen kare matasa da al’umma daga barazanar kwayoyi tare da karfafa masa guiwa wajen ci gaba da bibiyar masu safarar miyagun kwayoyi a sassa daban-daban na kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here