Tambuwal ya fice daga PDP zuwa ADC

Screenshot 2026 03 12 042829 750x430

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar ADC.

Tsohon gwamnan ya bayyana rikicin cikin gida na PDP da rashin jituwa a shugabanci da kuma ƙara tsananta rabuwar kai a cikin jam’iyyar a matsayin manyan dalilan da suka sa ya yanke wannan hukunci.

Tambuwal, wanda kuma ya taba zama kakakin majalisar wakilai, ya sanar da sauya shekar tasa a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X da safiyar ranar Alhamis, inda ya tabbatar da cewa ya rubuta takardar murabus dinsa zuwa ga shugaban jam’iyyar a mazabarsa kafin ya shiga ADC tare da abokansa da magoya bayansa.

Ya bayyana cewa bayan zurfin tunani da tattaunawa da mutane da dama, ya yanke shawarar a hukumance ya ajiye kasancewarsa dan jam’iyyar PDP, kuma ya aika da takardar murabus dinsa ga shugaban jam’iyyar a mazabarsa a rubuce.

Tambuwal ya amince cewa PDP ta taka muhimmiyar rawa a tafiyarsa ta siyasa, wadda ta hada da rike mukamin kakakin majalisar wakilai da kuma yin wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar Sokoto.

Sai dai ya ce rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar, rashin jituwa a shugabanci da kuma karuwar rarrabuwar kai sun sanya ya zama abu mai wahala ya ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa wadannan abubuwa sun raunana hadin kai da alkiblar da jam’iyyar ta taba kasancewa da su a baya, lamarin da ya tilasta masa daukar wannan mataki.

Da yake bayyana dalilin da ya sa ya zabi ADC a matsayin sabuwar jam’iyyarsa, Tambuwal ya ce yana da yakinin cewa jam’iyyar na da karfin zama wata mafita mai karfi ga cigaban dimokuradiyya a Najeriya.

Ya kara da cewa ya dauki wannan mataki ne bisa imaninsa cewa Najeriya na bukatar wata jam’iyya mai karfi wadda za ta ginu kan gaskiya, rikon amana, hada kai da kuma jajircewa wajen cigaban kasa.

Sauya shekar Tambuwal ta biyo bayan sauya shekar wasu fitattun ‘yan siyasa zuwa jam’iyyar, ciki har da tsohon dan takarar shugaban kasa Peter Obi, abin da ke kara nuna ADC a matsayin wata jam’iyyar adawa mai karfi yayin da ake tunkarar babban zaben ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here