Sojoji sun kama wanda ake zargi da safarar makamai da matarsa a Kaduna

Army keeps peace in Kaduna 680x430

Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Enduring Peace (JTF-OPEP) sun kama wani mutum da ake zargi da safarar makamai tare da matarsa a garin Saminaka, ƙaramar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba daga birnin Jos.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa rundunar JTF-OPEP an kafa ta ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato da wasu sassan jihohin Kaduna da Bauchi.

A cewar Manjo Zhakom, an cafke mutumin mai shekaru 40 da matarsa mai shekaru 18 ne a ranar 8 ga Oktoba, tare da haɗin gwiwar rundunar Operation Fansan Yamma (OPFY).

Ya ce an kama su ne a wani binciken tsaro da aka tsara don ƙarfafa tsaro a yankunan da rundunar ke aiki, inda jami’an JTF-OPEP da OPFY suka kafa shingen bincike a wajen garin Saminaka, inda aka tsayar da su.

Hakan kuwa ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu daga wata hukumar leƙen asiri ta jihar Filato, wanda ya kai ga gano su da kuma kwace harsasai guda 1,207 na nau’in 7.62 mm (Special).

An samu tabbacin cewa waɗannan harsasai na nufin isarwa ne ga ‘yan bindiga da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma na ƙasar.

A halin yanzu dai, waɗanda ake zargin da kuma kayayyakin da aka gano suna hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here