Sanata Barau ya karɓi ƴan NNPP Kwankwasiyya sama da 1,000 da suka sauya sheƙa zuwa APC a Kano

WhatsApp Image 2025 11 02 at 18.15.30 750x430

Fiye da mambobi dubu ɗaya na jam’iyyar (NNPP) tashin Kwankwasiyya a jihar Kano ne suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin.

Waɗanda suka sauya sheƙar, ƙarƙashin ƙungiyar Kwankwasiyya One Blood, sun bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne saboda ayyukan ci gaba da taimakon da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da Sanata Barau ke gudanarwa a Kano da wasu sassan ƙasar.

A cikin wata sanarwa da mai ba Sanata Barau shawara kan harkokin yaɗa labarai, Malam Isma’il Mudashir, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce mambobin sun taru ne a cibiyar Fine Time Events da ke cikin birnin Kano, inda suka jefar da hular su ja da ke zama alamar tafiyar Kwankwasiyya.

Shugaban ƙungiyar, Aminu Murtala Minjibir, ya bayyana cewa sun canza sunan ƙungiyarsu zuwa Barau Maliya One Blood, yana mai cewa sun yi aiki tukuru a baya don tafiyar Kwankwasiyya, amma sun lura cewa NNPP ba ta shirin bunkasa al’ummar Kano.

Ya ce mambobinsu suna ko’ina cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, kuma sun yanke shawarar shiga “jirgin nasara” wato APC, domin ci gaban jama’ar jihar.

Da yake karɓar mambobin, Sanata Barau ya ce matakin da suka ɗauka shi ne na gaskiya, yana mai cewa jam’iyyar NNPP ƙarama ce wadda ta taƙaita a wasu yankuna kaɗan na birnin Kano, yayin da APC ke jagoranci a matakin ƙasa da Afirka.

Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu yana ci gaba da tallafawa Kano da Arewa baki ɗaya, yana neman haɗin kai da addu’o’in jama’a don cigaban ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here