Rashin tsaro: Amurka ta tura sojoji zuwa Najeriya bayan hare-haren sama na watan Disamba

flck9kpTURBXy8xZjI0MmZjNDNiNDY0ZjYyMTMyM2Q4Njc4NzcyYjZkYi5qcGeSlQMAJ80FAM0C0JMFzQMWzQGu3gACoTAGoTEA 750x430

Ƙasar Amurka ta tura ƙaramin rukuni na sojoji zuwa Najeriya, wanda shi ne karon farko da rundunar sojin Amurka ta samu sahihin kasancewa a ƙasa tun bayan hare-haren sama da aka kai wa ’yan ta’adda a ranar Kirsimeti ta shekarar 2025.

Turo sojojin zuwa Najeriya ya biyo bayan hare-haren sama da Shugaba Donald Trump ya bayar da umarni a watan Disamba na shekarar 2025 kan wuraren da ya bayyana a matsayin sansanonin Daular Islama a cikin ƙasar.

Shugaba Trump ya kuma nuna cewa ana iya samun ƙarin matakan soji daga Amurka a Najeriya nan gaba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa Amurka na gudanar da jiragen sa ido a sararin samaniyar Najeriya daga ƙasar Ghana tun daga ƙarshen watan Nuwamba na shekarar 2025, domin tattara bayanan sirri gabanin hare-haren saman da aka kai a watan Disamba.

Rahoton Reuters ya nuna cewa turo sojojin ya biyo bayan yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da birnin Washington domin ƙara haɗin gwiwa wajen tunkarar ƙarin barazanar ta’addanci da ke ƙaruwa a yankin Yammacin Afirka.

Shugaban Rundunar Amurka ta Afirka, Janar Dagvin R. M. Anderson, ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa ya haifar da ƙarin aiki tare tsakanin ƙasashen biyu, wanda ya haɗa da turo ƙaramin rukuni na sojojin Amurka masu wasu ƙwarewa na musamman domin tallafa wa ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci a Najeriya.

Rahoton ya ƙara da cewa Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya tabbatar da kasancewar sojojin, yayin da majiyoyin tsaro suka bayyana cewa Amurkawa na taka rawa wajen tattara bayanan sirri da kuma taimaka wa sojojin Najeriya wajen kai hare-hare kan ƙungiyoyi kamar Boko Haram da Daular Islama ta Lardin Yammacin Afirka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here