NSCDC ta kama mutane 4 da ake zargi da satar wayoyi a Kano

IMG 20260313 WA0033 750x430

Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa NSCDC reshen jihar Kano ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da satar wayoyin hannu a wani samame da ta kai a Dorayi Babba da ke karamar hukumar Gwale a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SC Ibrahim Idris-Abdullahi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Kano.

Ya ce wadanda ake zargin, wadanda shekarunsu ke tsakanin 17 zuwa 27, duk suna zaune ne a Dorayi Babba kuma an kama su ne bisa zargin haddasa tashin hankali ga jama’a, kai hare-hare da kuma satar wayoyin hannu.

Ya kara da cewa an kama su ne bayan wani mutumin kirki ya kai rahoto ga ofishin NSCDC da ke yankin.

A cewarsa, mutumin da ya ba da rahoton ya sanar da jami’an tsaro cewa wasu gungun bata-gari dauke da makamai masu hadari sun taru a kusa da wata makarantar al’umma da ke Dorayi Babba, inda suke kai hare-hare ga masu ibada da ke gudanar da sallar Tarawihi da kuma masu wucewa.

Ya kara da cewa bata-garin suna kwace kayayyakin jama’a da suka hada da wayoyin hannu kafin daga bisani jami’an tsaro su kama su.

Ya bayyana cewa yayin samamen an kama mutane hudu bayan sun kai hari ga wani mutum tare da kwace wayarsa.

Idris-Abdullahi ya ce an kuma kwato wuka mai kaifi da kuma kunshi biyu na tabar wiwi daga hannun wadanda ake zargin lokacin da aka kama su.

Ya kara da cewa bincike kan lamarin ya kammala kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Rundunar ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar tare da bukatar mazauna jihar su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanai masu amfani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here