Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United ta ƙaryata tare da yin watsi da wani rahoton da aka wallafa a intanet game da abin da ya faru a lokacin wasan su na gasar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NPFL) da ƙungiyar Barau FC a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ta, Malam Nasir Gide, ya fitar a ranar Lahadi a Katsina, inda ya ce rahoton karya ne kuma yana yaudarar jama’a.
Ya bayyana cewa rahoton ya zargi magoya bayan ƙungiyar da mamaye fili, tare da samun tashin hankali, har ma aka ce an yanka wani ɗan wasa.
Gide ya ce waɗannan zarge-zargen basu da tushe, domin ƙoƙarin ɓata sunan ƙungiyar da wasanni a jihar ne kawai.
Ya ƙara da cewa a lokacin wasan babu wani magoyin baya da ya shiga filin wasa.
Ya amince cewa wasan ya kasance da ɗan zafi saboda wasu hukuncin alkalanci da suka jawo cece-kuce, amma jami’an tsaro sun kasance cikin shiri don tabbatar da tsaro har zuwa ƙarshen wasa.
Gide ya bayyana cewa ƙungiyar ta yi matuƙar takaici kan yadda wata kafar yaɗa labarai da ake girmamawa ta wallafa irin wannan labari mai girman gaske ba tare da tantance gaskiya ba.
Ya yi gargadin cewa irin waɗannan bayanan ƙarya na iya lalata martabar ƙungiyar da kuma kawo cikas ga ci gaban ƙwallon ƙafa a jihar da ƙasar baki ɗaya.
Ya jaddada cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United tana tsayawa kan ƙa’idojin sana’a, ladabi da kuma wasa cikin gaskiya a kowane lokaci.
Ƙungiyar ta kuma zargi Barau FC da yada wannan labarin ƙarya, tana mai cewa za ta bar hukumar kula da gasar (LMC) ta gudanar da bincike sannan ta ɗauki matakin da ya dace.
Gide ya ce ƙungiyar ta nemi kafar labarin da ta wallafa rahoton ta janye labarin tare da bayar da haƙuri a bainar jama’a, inda ya ƙara da cewa idan ba su yi hakan ba, ƙungiyar za ta ɗauki matakin shari’a don kare kanta.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wannan sanarwar ta fito ne domin fayyace gaskiyar lamari da kuma kare martabar ƙungiyar Katsina United a idon jama’a.












































