Hukumar kula da yanayi ta ƙasa NiMet ta yi hasashen cewa za a fuskanci hazo mai ƙura da kuma gajimare daga Lahadi zuwa Talata a sassan ƙasar nan.
Rahoton yanayin da hukumar ta fitar a Abuja ya nuna cewa a ranar Litinin ya nuna cewa, za a samu matsakaicin hazo mai ƙura a yankin arewa a duk tsawon lokacin hasashen.
Rahoton ya kuma nuna cewa za a samu hazo mai kauri a yankin tsakiyar ƙasa, yayin da biranen cikin ƙasar a yankin kudu za su fuskanci matsakaicin hazo mai ƙura.
A cewar hasashen, yankunan gabar teku za su ga hasken rana tare da ɗan gajimare, tare da yiwuwar tsawar ruwan sama kaɗan a wasu sassan jihohin Lagos, Bayelsa da Rivers daga baya ayi rana.
Hukumar ta nuna cewa a ranar Talata ma za a ci gaba da samun matsakaicin hazo mai ƙura a yankin arewa da tsakiyar ƙasa, haka nan biranen cikin ƙasar a yankin kudu za su fuskanci irin wannan yanayi.
Rahoton ya ƙara da cewa a ranar Laraba za a samu hazo mai kauri a yankin arewa, yayin da yankin tsakiyar ƙasa da biranen cikin ƙasar a yankin kudu za su ci gaba da samun matsakaicin hazo, amma yankunan gabar teku za su kasance da hasken rana tare da ɗan gajimare.
Hukumar ta ja hankalin jama’a da su ɗauki matakan kariya saboda ƙurar da ke shawagi a sararin samaniya, musamman masu fama da cututtukan numfashi, tare da shawarwarin yin taka-tsantsan wajen tuƙi da kuma neman cikakken rahoton yanayi ga kamfanonin jiragen sama domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.
NAN













































