Hukumar Kula da Ingancin Abince da Magunguna ta Najeriya NAFDAC ta ce ta lalata magungunan jabu da kayayyakin da kwatan watan lalacewarsu ya wuce, wanda kuɗinsu ya kai sama da miliyan 300 a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce an samu magungunan ne a wuraren ajiya tare da wasu shaguna a faɗi jihar da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
Yayin da yake magana da ‘yan jaridar jim kaɗan bayan lalata magungunan, babban daraktan hukumar ta NAFDAC Farfesa Moji Adeyeye ya bayyana sayar da waɗannan magunguan ga ‘yan ƙasa da cewa babbar cutarwa ce ga rayuwar ɗan adam.
Adeyeye wanda ya samu wakilcin daraktan bincike na hukumar Francis Ononiwu ya ce an ƙwato magungunan ne daga kamfanonin da ke samar da su da masu shigo da magungunan da kuma masu sayar da su, domin kare lafiyar ‘yan ƙasa.












































