Na yi wa ‘yan Najeriya duk abin da zan iya – Shugaba Buhari

FB IMG 16725691004867787
FB IMG 16725691004867787

Shugaban Najeriya Muhammadu ya shawarci ‘yan kasar da su shiga sabuwar shekarar 2023 da fatan ganin kasar ta ci gaba da fuskar hadin kai da fatan ci gaba.

Cikin sakonsa na sabuwar shekara da ya aika a jiya, Shugaba Buhari ya ce 2023 shekara ce da za a kara mayar da hankali kan harkokin tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma yakin da cin hanci.

Buhari wanda ya yi maraba da suka da yabon da ‘yan Najeriya ke yi masa, ya ce ya yi iya abin da zai iya ga mutanen kasar, yayin da yake fatan duk shugaban da zai zo ya dora daga inda ya tsaya, domin ciyar da Najeriya caga.

Ya ce dole yan Najeriya su dauki ragamar tabbatar da zabukan da za a yi a 2023 an yi su babu cuta babu cutarwa.

Ya kuma shawarci ‘yan kasar da su kiyaye da tayar da hankali a lokutan zabe, su kuma kiyaye daga duk wani dan siyasa da zai nemi su yi hakan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here