Sanata mai wakiltar yankin Abia ta Arewa, Orji Kalu, ya nemi majalisar dattawa ta sake duba dokar rundunonin soji domin magance abin da ya kira “asara ga ƙwararrun sojoji” sakamakon naɗin shugabannin rundunonin tsaro daga cikin ƙanana ajin horo.
Kaki ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin zaman majalisar, inda ya bayar da gudunmawa a tattaunawar dokar da ke neman soke tsohuwar dokar sojoji da kuma kafa sabuwa.
Kalu ya bayyana cewa yin naɗin shugabannin sojoji daga ƙanana da nasu wuce ajin karatu na rundunonin soja ba, yana tilasta wa manyan hafsoshi yin murabus da wuri, abin da ke janyo asarar ƙwararrun ma’aikata da kuma kuɗaɗen jama’a da aka kashe wajen horas da su.
Ya ce dole a yi gyara a tsarin don tabbatar da cewa duk naɗin shugabannin sojoji yana bin tsarin ajin karatu domin tabbatar da adalci da ɗorewar aiki.
Sanatan ya kuma bayyana cewa idan shugaban ƙasa yana son naɗa shugaban rundunar sojojin ƙasa, na ruwa, ko na sama, to dole a bi tsarin ajin karatu domin kowane aji ya samu damar jagoranci.
Ya kara da cewa a wasu lokuta ana samun naɗin mutum ɗaya wanda ke haifar da murabus ɗin hafsoshi sama da dari biyu waɗanda har yanzu suna da shekaru da dama kafin ritaya, abin da ya kira asara ga ƙasar da kuma rashin adalci.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya gargadi takwarorinsa su yi taka-tsantsan wajen tsara sabuwar dokar don kada ta keta hurumin shugaban ƙasa bisa tsarin mulki.
Ya bayyana cewa rundunonin soji na da nata tsarin aiki, kuma shugaban ƙasa yana da hurumin yin naɗe-naɗe bisa yadda tsarin yake, don haka dole ne majalisar ta yi la’akari da duka bangarorin biyu wajen yin gyaran dokar.
Majalisar ta amince da dokar da sanata Abdulaziz Yar’Adua, mai wakiltar yankin Katsina ta tsakiya, ya gabatar, bayan ta tsallake karatu na biyu.












































