Matatar Man Fetur ta Dangote ta tabbatar da cewa ta kori wasu daga cikin ma’aikatanta, duk da cewa ta ce ƙalilan ne abin ya shafa, a wani shiri na sake fasalin harkokin gudanarwa.
Hakan na cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce an ɗauki wannan mataki ne don kare matatar daga yawan munanan hare-hare na cikin gida da ke kawo barazanar tsaro da rage ingancin aiki.
Kamfanin ya ce sama da ma’aikata 3,000 ‘yan Najeriya ne ke ci gaba da aiki a halin yanzu, kuma kaɗan daga cikinsu abin ya shafa.
Ya kuma kara da cewa yana ci gaba da ɗaukar sababbin ma’aikata ta hanyar shirye-shiryen horas da matasa da kuma ɗaukar ƙwararru.
Sanarwar ta jaddada cewa matatar na mutunta ƙa’idojin aikin duniya, ciki har da ’yancin ma’aikata na shiga ƙungiya ko akasin haka.
Karin labari: Gwamnatin tarayya ta gayyaci Ɗangote da shugabannin NUPENG kan batun yajin aiki
Sai dai ƙungiyar manyan ma’aikatan Man fetur da iskar Gas (PENGASSAN) ta zargi kamfanin da kora ma’aikatan Najeriya bayan sun shiga ƙungiyar.
A cewar ƙungiyar, hakan ya saba wa ’yancin ma’aikata da kundin tsarin mulki, tare da bayyana shi a matsayin barazana da tsoratarwa.
Ƙungiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne cikin sa’o’i 24 bayan kafa kwamitin rikon kwarya na reshen ƙungiyar da kuma mika sunayen farkon waɗanda suka yi rijistar shiga ƙungiyar ga shugabancin kamfanin.
PENGASSAN ta ce a ranar 25 ga Satumba 2025 aka yi taro da ma’aikatan, inda yawanci suka tabbatar da shiga ƙungiyar.
Sai dai da maraicen ranar nan, an fara tsoratar da su, ciki har da janye motocin ɗaukar ma’aikata, wanda ya tilasta musu biyan har naira 4,000 don zuwa wurin aiki.













































