Kano: Masu filaye a Dangoro sun koka kan rashin kyakkyawan wakilci a ganawarsu da jami’an gwamnati

WhatsApp Image 2025 11 13 at 11.12.12 750x430

Wasu masu filaye a unguwar Dangoro da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda aka gudanar da taro tsakanin su da jami’an gwamnati kan rikicin ƙasa da ke faruwa a yankin, suna masu cewa basu ga kyakkyawan wakilci yadda ya kamata ba.

Taron ya gudana ne a sakatariyar ƙaramar hukumar Kumbotso, inda wakilan ‘yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya DSS, jami’an ma’aikatar kula da ƙasa da tsare-tsaren birane, da kuma masu riƙe da muƙaman gargajiya suka halarta.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa masu filayen sun zargi dagacin yankin, Ishaq Yusuf Ishaq, da ƙin sanar da su taron duk da cewa sun taɓa neman ganawa da shi kan batun ƙasa da ake rikici a kai, inda suka ce yana goyon bayan gwamnati maimakon kare muradun jama’arsa.

Mataimakin shugaban ƙungiyar masu gonaki, Sunusi Haruna, ya bayyana cewa sun samu labarin taron ne bayan an riga an fara shi, kuma kafin su isa wajen taron an gama, abin da suka ce wata dabara ce ta hana su bayyana ra’ayinsu a tattaunawar da ta shafi makomar filayensu.

Labari mai alaƙa: Masu Gonaki da Filaye sun gudanar da Sallar Al’ƙunuti kan yunƙurin gwamnati na sake kwace musu kadarori don gina sabuwar kasuwa

Masu gonakin sun bayyana cewa rashin sanar da su taron ya saba da adalci da gaskiya, kuma yana nuna gazawar jagoranci daga wanda ya kamata ya kasance mai kare jama’a.

Sun ce nuna adalci da wakilci na gaskiya ga jama’a ba tawaye ne ga gwamnati ba, illa nuna shugabanci na gari.

A baya-bayan nan ma, mazauna Dangoro sun gudanar da addu’a ta musamman domin neman taimakon Allah kan abin da suka bayyana a matsayin ci gaba da kwace filayen su don shirye-shiryen gwamnati, musamman batun mayar da kasuwar ‘Yan Lemo da ta kayan lambu ta Yankaba zuwa yankinsu.

A yayin taron, wani mai gona mai suna Haruna Muhammad ya bayyana damuwarsa cewa shirin gwamnati na iya jefa mutane cikin wahala, musamman ma wadanda suka gada tun daga iyayensu.

Wani dattijon al’umma, Alhaji Gambo Saminu Adamu, ya roƙi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya sa baki cikin lamarin, yana mai cewa suna da tabbacin adalcin gwamnan wajen magance rikicin cikin gaskiya da tausayi.

Sakataren ƙaramar hukumar Kumbotso, Abubakar Bala Sheka, ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa gwamnati ba ta da niyyar kwace ƙasar jama’a da karfi, domin shirin kasuwar sabuntawa ne na ci gaba.

Sai dai duk da wannan bayanin, masu gonaki da filaye sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da neman adalci da tabbatar da cewa ana ba su damar wakiltar kansu a duk wata tattaunawa da ta shafi ƙasashensu da rayuwarsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here