Majalisar Wakilai ta fara bincike kan tallafin kiwon Lafiya na Dala Biliyan 4.6

Reps new 750x430

Majalisar wakilai ta fara sauraren bincike kan yadda aka gudanar da sama da Dala Biliyan 4.6 da Najeriya ta karɓa daga Asusun Tallafin Ƙasa da kuma Hukumar (USAID) ta Amurka tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.

An bayar da tallafin ne domin ya taimaka wajen yaƙi da cututtukan HIV/AIDS, tarin fuka (TB), da zazzabin cizon sauro, tare da ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar ƙasa.

Majalisar ta buɗe zaman sauraren binciken a birnin Abuja ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar, Ɗan majalisa Tajudeen Abbas, wanda mataimakinsa Ibrahim Isiaka ya wakilta.

Shugaban kwamitin majalisar kan cututtukan da ke yaduwa, Ɗan majalisa Amobi Ogah, ya bayyana cewa binciken na nufin tabbatar da cewa an yi cikakken bayani kan kowanne kuɗi da aka kashe.

Ya ce ba za a ci gaba da karɓar tallafi da ke hana Najeriya ikon sarrafa kudaden ba, domin kowace gudunmawa da ake bayarwa dole ta bai wa ƙasar damar kula da yadda ake amfani da ita.

Ogah ya ce duk da Biliyoyin da aka kashe wajen yaƙi da cututtuka masu yaduwa, ƙasar har yanzu tana fama da nauyin cututtukan HIV/AIDS, TB da zazzabin cizon sauro.

Ya kuma bayyana cewa za su yi aiki tare da Hukumar Yaƙi da masu yiwa ƙasa ta’annati (EFCC) da Hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa (ICPC) domin tabbatar da cewa dukkan masu aiwatar da shirye-shiryen tallafin sun ba da cikakken bayani.

Kwamitin ya kuma sanar da shirin wajabta cewa dukkan masu karɓar tallafin su rika gabatar da tsare-tsaren ayyukansu ga majalisar kafin a sake raba wani sabon tallafi.

Ya kuma ce, an kammala shirye-shirye na sake fasalin Hukumar Yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki ta ƙasa (NACA) zuwa Hukumar Kula da Cutar Kanjamau, Tarin Fuka da Zazzabin Cizon Sauro (NACATAM), domin ƙara inganta kulawa da wadannan manyan cututtuka uku.

Taron ya haɗa da halartar ministan lafiya mai kula da harkokin tsare-tsare, Farfesa Muhammad Ali Pate, darakta-janar na NACA, wakilan Asusun Tallafin Ƙasa, USAID, ƙungiyoyin fararen hula da hukumomin yaƙi da cin hanci. An gudanar da shi ne domin ƙarfafa gaskiya, ɗorewar amana da kuma ikon Najeriya kan shirye-shiryen lafiyarta.

Minista Pate ya bayyana goyon bayansa ga binciken, inda ya ƙarfafa Najeriya da ta fara ɗaukar nauyin kuɗaɗen lafiyarta yayin da tallafin ƙasashen waje ke raguwa.

Ya kuma ce, duk da cewa tallafin ƙasashen waje ya ceci rayuka da dama, har yanzu kuɗin da Najeriya ke warewa don kiwon lafiya bai kai matsayin da aka tsara a Yarjejeniyar Abuja na kashi 15 cikin ɗari ba.

Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa wannan binciken na nuna jajircewar majalisar wajen tabbatar da gaskiya a cikin kuɗaɗen kiwon lafiya, inda ya yi alkawarin samar da rahoton da ke da hujja kan yadda aka yi amfani da tallafin da kuma tasirinsa ga lafiyar jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here