Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Tinubu na ciyo rancen Naira Tiriliyan 1.15

Senate 1 750x430

Majalisar Dattawa Najeriya ta amince da bukatar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na neman rancen cikin gida na Naira Tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025.

Amincewar ta biyo bayan karɓar rahoton kwamitin majalisar dattawa kan lamunin cikin gida da na ƙasashen waje da mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Manu Haruna daga jam’iyyar APC ta jihar Taraba, ya gabatar.

Shugaban ƙasa Tinubu ya aika da buƙatar rancen a ranar 4 ga Nuwamba, inda ya nemi majalisar ta ba da izinin karɓar lamuni domin cike gibin da aka samu a kasafin kuɗin shekarar 2025.

Majalisar Dattawa bayan karɓar buƙatar ta umarci kwamitin lamuni da sauri ya yi bitar lamarin tare da kawo rahoto ga zauren majalisar.

A cikin rahoton, Sanata Haruna ya bayyana cewa kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka amince da shi ya kai Naira Tiriliyan 59.99, wanda ya fi na farko da gwamnati ta gabatar na Tiriliyan 54.74 da Tiriliyan 5.25. Wannan karin ya jawo giɓin kasafi da ya kai Tiriliyan 14.10, yayin da adadin lamunin da aka tsara a cikin kasafin ya kai Tiriliyan 12.95, abin da ya haifar da giɓin da ba a rufe ba na Tiriliyan 1.147.

Sanata Haruna ya ce saboda haka akwai buƙatar ƙara iyakar rancen cikin gida da naira Tiriliyan 1.147 domin rufe gibin.

Ya kuma shawarci majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban ƙasa domin tabbatar da cikar kasafin kuɗin shekara.

Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi ya jaddada muhimmancin aiwatar da shawarwarin kwamitin, inda ya bukaci kwamitin kasafi da ya yi aiki tare da ofishin kula da bashi da kuma ofishin kasafi domin tabbatar da isasshen tanadi wajen biyan kasafin.

Sanata Adeola Solomon daga jihar Ogun ya yaba wa kwamitin bisa ingancin rahotonsa, yana mai cewa ya dace da abin da ya faru a lokacin da aka tsara kasafin kuɗin.

Ya kuma ce, akwai buƙatar shirya yadda za a samo kuɗin cikin gaggawa domin ci gaba da aiwatar da kasafin, musamman ɓangaren manyan ayyuka.

Bayan amincewa da rancen, majalisar Dattawa ta umurci ma’aikatar kuɗi ta tarayya da ofishin kula da bashi da su gudanar da ɗaukar rancen cikin iyakokin da aka amince da su, tare da tabbatar da gaskiya, bayyanawa da dorewa a cikin yarjejeniyar.

Haka kuma, majalisar ta umarci kwamitin lamunin cikin gida da na waje da ya sa ido kan yadda za a yi amfani da kuɗin da aka amince da su, tare da karɓar rahotanni a kowane wata daga ma’aikatar kuɗi da ofishin kula da bashi kan yadda ake amfani da kuɗin da kuma tsarin biyan su.

Shugaban majalisar Dattawa na wucin gadi, Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano, wanda ya jagoranci zaman, ya yaba wa kwamitin bisa yadda ya gudanar da aikinsa cikin kankanin lokaci, yana mai cewa rahoton ya fito fili kuma yana da inganci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here