Mahaifiyar Gwamnan Katsina Dikko Radda ta rasu

9dfa1e90 09a5 4a42 8842 aac63097d477.jpg

Mahaifiyar gwamnan Katsina, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, ta rasu tana da shekara 93.

Fadar gwamnatin jihar ce ta sanar da rasuwar mahaifiyar Gwamna Dikko Umaru Radda a yau Lahadi cikin wata sanarwa amma ba ta bayyana musabbabin rasuwar tata ba.

Sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai Ibrahim Kaula Mohammed ya sanya wa hannu ta ce za a yi jana’izar marigayiyar da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.

“Daga cikin ‘ya’yan da ta bari akwai mai garin Radda Kabir Umar Radda, da Hauwa Umar Radda, tsohuwar matar tsohon shugaban Najeriya marigayi Umar Musa Yar’adua,” in ji sanarwar.

Za a yi jana’izar a garin Radda mai nisan kusan kilomita 70 daga Katsina babban birnin jihar.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here