Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta hana gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa tsayawa takarar sake zama gwamna a zaben shekarar 2028.
Yayin yanke hukunci a ranar Alhamis, mai shari’a Toyin Bolaji Adegoke ta bayyana cewa kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima bai amince shugaban kasa ko mataimakinsa, gwamna ko mataimakin gwamna su ci gaba da rike mukami sama da shekaru takwas ba.
Aiyedatiwa ya fara shan rantsuwa a matsayin gwamna a ranar 27 ga Disamba 2024 bayan rasuwar wanda ya gada Oluwarotimi Akeredolu domin kammala wa’adin mulkinsa da ya rage.
Daga bisani kuma an sake rantsar da shi a ranar 24 ga Fabrairu 2025 bayan ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 16 ga Nuwamba 2024.
Shari’ar ta samo asali ne daga wani mamba na jam’iyyar APC a jihar Ondo mai suna Kin Egbuwalo wanda ya kalubalanci cancantar gwamnan na sake tsayawa takara a wani wa’adi.
Ta hannun lauyansa Adeniyi Akintola, SAN, mai karar ya bukaci kotu ta yi fassarar sashe na 137(3) na kundin tsarin mulkin 1999 dangane da cancantar gwamna Aiyedatiwa ya nemi wa’adi na biyu.
Wadanda aka shigar kara sun hada da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, gwamna Aiyedatiwa, jam’iyyar APC da kuma mataimakin gwamnan jihar Olayide Adelami.
Mai shari’a Adegoke ta bayyana cewa takardun da mai kara, wanda ake kara na farko da kuma wanda ake kara na biyu suka gabatar ne kawai za a yi la’akari da su, inda ta ce takardun wadanda ake kara na uku zuwa na biyar sun zama kamar an yi watsi da su saboda ba su halarci sauraron karar ba.
Kotun ta kuma yi watsi da korafin da wanda ake kara na farko ya gabatar, tana mai cewa karar ba ta da alaka da zato ko nazari kawai, kamar yadda wadanda ake kara na farko da na biyu suka yi ikirari, domin kuwa tana da ingantaccen dalilin shigar da ita.
Mai shari’ar ta kara da cewa barin gwamnan ya sake tsayawa takara ya kuma yi wani wa’adin shekaru hudu zai saba da matsayar kotun koli a shari’ar Marwa da Nyako wadda ta tabbatar da cewa shugaban kasa ko gwamna ba zai iya ci gaba da rike mukami sama da shekaru takwas ba.
Saboda haka kotun ta yanke hukuncin cewa karar mai kara tana da tushe, kuma ta amince da dukkan bukatun da ya gabatar.












































