Kamfanin mai na ƙasa NNPC ya rage farashin man fetur a gidajen sayar da man sa zuwa Naira 1,130 kan kowace lita a Lagos da kuma Naira 1,165 kan kowace lita a Abuja.
Ragin farashin wanda ya fara aiki ranar Laraba ya nuna saukar Naira 100 daga farashin baya na Naira 1,230 kan kowace lita a Lagos da kuma saukar naira 95 daga Naira 1,260 kan kowace lita a Abuja.
A Lagos, an lura da sabon farashin a gidajen sayar da man NNPC da ke kan titin Isheri Oshun Road, Apple Junction da kuma Ago Palace Way.
Haka kuma a Abuja, kamfanin mai na ƙasa ya daidaita farashin sayar da man zuwa naira 1,165 kan kowace lita a gidajen sayar da man sa da ke Jabi da Wuse.
Ragin farashin ya zo ne duk da cewa har yanzu masu kasuwancin mai ba su nuna saukar da aka samu kwanan nan a farashin man fetur na gantry da matatar Mai ta Dangote ta rage ba.
Matatar Dangote a baya ta rage farashin gantry da Naira 100 kan kowace lita zuwa Naira 1,075 bayan farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya ragu zuwa kusan Dala 88 kan kowace ganga daga dala 110 kan kowace ganga.
Tashin farashin ɗanyen mai a baya ya samo asali ne sakamakon rikicin da ya kunno kai a Gabas ta Tsakiya tsakanin ƙasar Amurka da Iran da kuma Isra’ila wanda ya kawo cikas ga samar da mai tare da janyo fargabar yiwuwar toshe mashigar jiragen ruwa ta Strait of Hormuz.
Sai dai farashin mai ya fara raguwa bayan shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa rikicin na iya ƙarewa nan ba da jimawa ba, abin da ya rage fargabar tsaikon da ka iya shafar samar da mai a duniya.
Bayanai daga kasuwa sun kuma nuna cewa Brent crude, wanda shi ne ma’aunin farashin mai a duniya, ya ragu da kusan kashi 8.45 cikin ɗari zuwa kusan Dala 92 kan kowace ganga daga dala 110 kan kowace ganga.
Ragin ya biyo bayan tarurrukan ministocin ƙasashen Turai da suka tattauna yiwuwar sakin ajiyar mai domin taimakawa wajen daidaita farashin mai a kasuwar duniya.













































