Jami’ar UNIABUJA ta naɗa sabon shugaba

UniAbuja New scaled

Majalisar gudanarwa ta jami’ar Yakubu Gowon (tsohuwar jami’ar Abuja) ta amince da naɗin Farfesa Hakeem Babatunde Fawehinmi a matsayin sabon shugaban jami’ar.

Sanarwar naɗin ta fito ne yayin taron majalisar karo na 80 na musamman a ranar Juma’a, kamar yadda shugaban sashen yada labarai na wucin gadi na jami’ar, Dakta Habib Yakoob, ya bayyana.

Sanarwar ta ce wannan naɗi zai fara aiki daga ranar Talata 10 ga watan Fabrairu, 2026, kuma zai kasance na shekara biyar ne kacal, ba tare da damar sabuntawa ba.

A halin yanzu, Farfesa Fawehinmi shi ne mataimakin shugaban jami’ar Nigerian British University kuma an naɗa shi bayan wani lokaci da jami’ar ta yi ƙarƙashin shugabancin jami’ar na wucin gadi da gwamnatin tarayya ta naɗa, bayan rikicin da ya biyo bayan naɗin tsohuwar shugabar jami’ar, Farfesa Aisha Maikudi.

Haka kuma, majalisar ta amince da tsawaita wa’adin zaman Farfesa Mathew Adamu a matsayin shugaban jami’ar na wucin gadi har zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, 2026.

A cewar sanarwar, an fara naɗa shi a wannan matsayi ne daga gwamnatin tarayya a ranar 11 ga watan Agusta, 2025.

Farfesa Fawehinmi ya taka muhimmiyar rawa a harkokin ilimi da gudanarwa, inda ya taba zama kasance Shugaban Sashen Nazarin Halittar jiki karo biyu (2005 – 2007; 2007 – 2009), Associate Dean (2010 – 2012) da Dean (2012 – 2014) na tsangayar ilimin harhada magunguna (2012 – 2014). – 2020) na Jami’ar Fatakwal.

Ya kasance memba a kwamitoci daban-daban na jami’a, tare da taka rawa a ƙungiyoyin ƙwararru na cikin gida da na ƙasashen waje, ciki har da ƙungiyar likitocin Nijeriya, da ƙungiyar masana ilimin halittar jiki ta ƙasa, da sauran ƙungiyoyi.

Haka kuma, ya samu lambobin yabo da dama na kimiyya da hidimar al’umma, yana da gurbi a cikin cibiyoyin ilimi na ƙasa da ƙetare, kuma ya lashe lasisin gwamnatin tarayya kan kirkirar kujerar AMRG Anthropometry don auna sassan jikin ɗan adam.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here