Jami’an ‘yan sanda 5 da suka dawo daga zaben Edo sun mutu, wasu 11 sun jikkata a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a Kano

FRSC Accident

Rundunar ‘yan sanda a Kano ta tabbatar da mutuwar jami’an ‘yan sanda biyar a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Karfi da ke karamar hukumar Kura ta jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce wasu jami’an ‘yan sanda 11 sun samu raunuka a hadarin.
Ya ce hatsarin ya afku ne a kauyen Karfi da ke karamar hukumar Kura yayin da jami’an su ke dawowa Kano daga wani aiki na hukuma.
“Hatsarin ya faru ne a Karfi mai tazarar kilomita kadan zuwa Kano kuma biyar daga cikin jami’an sun mutu sakamakon hadarin yayin da wasu 11 suka samu raunuka.

“An tattaro cewa motar da jami’an ‘yan sandan ke ciki ta yi karo da wata tirela a kauyen.
“Jami’ai biyar ne suka mutu nan take yayin da wasu 11 da suka samu raunuka daban-daban aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Mohammed inda a yanzu haka suke samun kulawar likitoci”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here