
Kungiyar ’yan ta’adda ta ISWAP ta kori tsoffin ’yan kungiyar Boko Haram wadanda a baya suka sauya sheka suka kuma yi mubaya’a gareta, bayan rasuwar shugabansu, Abubakar Shekau.
Aminiya ra rawaito cewa Abubakar Shekau, tsohon Shugaban Boko Haram, ya kashe kansa a wata arangama da wasu manyan kwamandojin ISWAP da suka sauya sheka a watan Yunin 2021.
Sakamakon haka, a ranar 24 ga watan Janairu, ISWAP karkashin jagorancin Ba’a Shuwa, ta kai hare-hare a matsugunan Boko Haram a Mantari, Gabchari da Maimusari a yankin Bama, inda suka kashe mayakan da dama tare da tilasta wa wasu tserewa zuwa yankin Banki.
Aminiya ta gano cewar, tsoron halaka su a fagen fama ya tilasta wa kwamandojin Boko Haram da iyalansu barin aikinsu tare da mika wuya ga sojoji.
Da yawa daga cikin mayakan sun kuma mika makamansu sakamakon tsananin yunwa da kuma kusan rashin samun damar shan magunguna ko cin abinci na yau da kullun.
A bisa dukkan alamu dai karfin fadan nasu ya ragu matuka inda ragowar suka bar sansanoni daban-daban, inda suka bar wasu ’yan ta’adda wadanda ba su da wata dama ta ko dai sojojin Najeriya ko kuma su kansu ’yan ta’addan gudun rasa ransu.












































