Ƙasar Iran, ta harba makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka da ke Qatar da Iraqi a yammacin yau Litinin, kamar yadda kafar yada labarai ta kasar ta rawaito, a wani abin da gidan talabijin din kasar ya kira mayar da martani ga harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan wasu muhimman wuraren nukiliyar Iran.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Iran IRNA, ya ruwaito cewa, an fara kai hare-haren makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka da ke Qatar da kuma a Iraqi, kuma ana kiran sa da sunan ‘Albarkacin Nasara’.
‘Yan jaridar AFP sun ruwaito cewa sun ji karar fashewar wasu abubuwa a Doha, babban birnin kasar Qatar, wanda ke da sansani mafi girma na Amurka a yankin.
A halin da ake ciki kuma, Qatar ta ce ta yi nasarar dakile wani harin makami mai linzami da Iran ta kai yau Litinin a sansanin Al Udeid na Amurka, Wanda ya kasance cibiyar sojin Amurka mafi girma a Gabas ta Tsakiya.
“Ma’aikatar tsaron kasar ta sanar da cewa, sojojin tsaron saman Qatar sun yi nasarar dakile wani harin makami mai linzami da aka kai kan sansanin jiragen sama na Al Udeid,” in ji sanarwar, inda ta kara da cewa “al’amarin bai yi sanadin mutuwa ko jikkata kowa ba”.
AFP













































