hallara yayin da BIKOBA ke gudanar da babban taron ta na shekara karo na 41

WhatsApp Image 2025 12 10 at 15.06.08 554x430

Shugabanni fitattu da tsofaffin ɗalibai za su hallara yayin da Kungiyar Tsofaffin Dalibai na Birnin-Kudu (BIKOBA) ke shirya taron shekara-shekara na 41 a ranar Addabar.

Yayin taron za a tarbi manyan baki, shugabannin gargajiya da tsofaffin ɗalibai daga sassa daban-daban na ƙasar nan a Birnin-Kudu a ranar Asabar yayin da Kungiyar Tsofaffin Dalibai na Birnin-Kudu (BIKOBA) ke gudanar da taron shekara-shekara na 41.

Taron zai gudana a Makarantar Unity College, wadda a da ake kira Kwalejin Birnin-Kudu, inda za a haɗa tsofaffin ɗalibai domin nazarin ayyukan ƙungiyar, tunawa da nasarori, tare da tattauna abubuwan da suka fi muhimmanci a sabuwar shekara.

Wani muhimmin ɓangare na taron shi ne jawabin jama’a da Alhassan Mohammed, mataimakin darakta a Babban Bankin Najeriya CBN, zai gabatar kan batun inganta ci gaban sana’a ta hanyar fasahar bayanai, domin fayyace yadda ƙwarewar fasahar zamani ke ƙara muhimmancin ƙwararru a duniyar aiki mai sauyawa.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Hashim Ubale Yusuf shi ne zai jagoranci zaman, yayin da gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, zai halarta a matsayin babban bako na musamman. Tsoffin gwamnonin Kano da Jigawa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Alhaji Sule Lamido, su ma za su kasance a wajen a matsayin manyan baƙi.

Ana sa ran zuwan fitattu daga cikin tsofaffin ɗaliban, ciki har da sanannen attajiri na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, da Sanata Mustafa Habeeb, waɗanda za su kasance cikin mahalarta.

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda shi ma ɗan wannan makaranta ne, zai kasance uban taro, yayin da shugaban ƙasa na ƙungiyar BIKOBA, Alhaji Ja’afar Usman Muhammad (Turakin Gaya), zai kasance babban mai masaukin baki.

A wannan shekarar, taron zai kunshi bayar da lambar yabo, amincewa da rahoton kuɗin shekara, da tattaunawa kan shirin ci gaban ƙungiyar, tare da halartar sarakunan gargajiya, masu tsara manufofi, shugabannin al’umma da wakilan ɓangaren ilimi, lamarin da ya sa taron ya zama ɗaya daga cikin mafi muhimmanci a tarihin haɗuwar tsofaffin ɗalibai a ‘yan shekarun nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here