Gwamnatin tarayya ta amince da bayar da Naira Biliyan Biyu ga kowace makaranta a matsayin kudin fara aiki ga kwalejin fasaha ta tarayya Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja da kuma jami’ar kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Epe a jihar Lagos, a wani bangare na kokarin tallafa wa fara gudanar da ayyukansu.
Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin kaddamar da manyan jami’an da aka nada domin jagorantar cibiyoyin biyu, kamar yadda tashar labarai ta Arise ta rawaito.
Daga cikin wadanda aka kaddamar akwai Farfesa Nosiru Onibon wanda zai zama shugaba na farko na makarantar fasaha ta tarayya Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja; Farfesa Adeola Oshikoya wanda aka nada a matsayin shugaban jami’a na jami’ar kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Epe; da kuma Dakta Angela Ajala wadda ta fara aiki a matsayin babbar sakatariya ta hukumar kula da kwalejojin ilimi ta kasa.
Yayin mika takardun nadin a Abuja, Alausa ya ce sabbin cibiyoyin ilimin an kirkiro su ne a matsayin wani bangare na kokarin gwamnatin tarayya na fadada damar samun ilimi mai zurfi da kuma karfafa karfin Najeriya a fannonin kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire.
Ya bayyana cewa duk wani yaro a wannan kasa ya cancanci samun ilimi mai inganci wanda zai iya yin gogayya da ka’idojin duniya, yana mai cewa an zabi wadanda aka nada ne bisa tarihin ayyukansu da nasarorin da suka samu a cibiyoyin ilimi na Najeriya.
Ministan ya kara da cewa idan aka ba mutum alhaki mai yawa, ana kuma sa ran zai yi aiki mai yawa, yana mai cewa an zabi su ne daga cikin Miliyoyin ‘yan Najeriya domin su yi wa kasarsu hidima, kuma wannan girmamawa ta shafi iyalansu ma.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na mai da hankali wajen gina tsarin ilimi mai karfi wanda zai samar da kwararrun ma’aikata da ake bukata domin ci gaban kasa.
A cewarsa, kudin fara aiki na Naira Biliyan Biyu da aka amince da su ga kowace cibiyar an tanade su ne domin taimakawa makarantu wajen kafa muhimman tsarin gudanarwa da na ilimi yayin da suke fara ayyukansu.
Alausa ya bukaci sabbin jami’an da aka nada su samar da ingantaccen shugabanci wanda zai tsara martaba da kuma ci gaban cibiyoyin na dogon lokaci.
Ya ce jami’ar kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Epe da makarantar fasaha da ke Abuja an kafa su ne a wurare masu muhimmanci domin amfani da damar tattalin arziki da kuma karfin bil’adama da ke wadannan yankuna.
Ministan ya kara da cewa ana sa ran cibiyoyin za su mayar da hankali kan fannonin kirkire-kirkire na fasaha, makamashi mai sabuntawa, magance sauyin yanayi, sarrafa hadarin bala’o’i da sauran fannonin bincike da suka shafi ci gaban kasa.
Haka kuma ya taya Ajala murna kan nadin da aka yi mata a matsayin babbar sakatariya ta hukumar kula da kwalejojin ilimi ta kasa, yana mai jaddada muhimmancin ilimin koyar da malamai ga ci gaban tsarin ilimin kasar.













































