Gwamnatin kwara tayi barazarar dawo da Dan kwangilar da yayi wata gada rubage

images 2 9
images 2 9

Gwamnatin jihar Kwara ta yi barazanar cewa za ta umurci wani dan kwangilar da ya gina gadar karkashin kasa akan Naira Miliyan Dubu 3 a garin Ilorin.

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin da ta shude ce ta Gwamna Abdulfatai Ahmed ce ta gina gadar saman wadda ke kofar shiga babban birnin jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai a lokacin da yake duba bangaren aikin da bai kammalu ba, kwamishinan ayyuka na jihar, Rotimi Ilyasu, ya ce gwamnatin jihar za ta kuma yi bincike ga wadanda abin ya shafa.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar za ta gyara wannan mummunar hanya a matsayin wani bangare na aikin da ta ke da shi a kan madafun iko, inda ya ce gyaran zai kawar da irin wahalhalun da asarar rai da mutanen da ke bin hanyar.

Kwamishinan wanda ya kara da cewa kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gina titin ba suda inganci kuma ci gaban da aka samu ya haifar da ragargajewar hanyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here