Gwamnatin jihar Katsina ta rufe wasu gidajen mai da ake zargi da hannu wajen sayar da man ga ‘yan fashin daji.
Hakan na zuwa ne sakamakon wani samame da kwamitin aiki da cikawa mai sa ido kan hauhawar farashi da zirga-zirga ya kai gidajen man, inda har aka kama mutum 10.
Karin labari: Jiragen sojin saman Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 30 a Borno
Katsina ta jima tana fama da hare-haren ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.