Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta nesanta kanta daga wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta dangane da aikin sake gina hanyar Alu Avenue da ke Nasarawa GRA, inda ta bayyana saƙon a matsayin ƙarya, ruɗani da kuma wanda ba ta amince da shi ba.
Wannan bayanin ƙaryatawar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir M. Hashim, ya sanya wa hannu a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa saƙon bai fito daga ma’aikatar ba kuma an jingina shi da ofishinsa ba bisa ka’ida ba.
Ma’aikatar ta ce saƙon da ke yawo ya yi ƙoƙarin nuna matsayar hukuma kan aikin, da ke ɗauke da suna da sa hannun kwamishinan ba bisa ka’ida ba.
Ta jaddada cewa wannan saƙo ba ya wakiltar matsayar ma’aikatar ko ta Gwamnatin Jihar Kano.
A cewar sanarwar, an yi cikakken tuntuba da haɗin gwiwa da dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomin da abin ya shafa kafin fara aikin sake gina hanyar Alu Avenue, musamman Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi da kuma Ma’aikatar Ayyuka.
Kwamishinan ya bayyana cewa an gudanar da cikakken binciken fasaha da na muhalli tare kafin a fara aikin.
Dakta Hashim ya ce matsayar gwamnati a bayyane take, inda ya jaddada cewa “ba a amince da sare ko itace ɗaya ba a kan hanyar Alu Avenue domin aikin sake gina hanyar.”
Sai dai ya bayyana cewa wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun sare itatuwa uku ba bisa izinin gwamnati ba, yana mai bayyana hakan a matsayin abin takaici da kuma abin da ba za a amince da shi ba.
Kwamishinan ya ce ma’aikatar ta yi Allah wadai da wannan aiki, tare da fara ɗaukar matakan shari’a da suka dace a kan waɗanda ke da hannu a lamarin.
Ma’aikatar ta kuma yi gargaɗi cewa ba za a sare ko itace ɗaya a kan hanyar Alu Avenue ko wata hanya a jihar ba tare da cikakken izinin gwamnati da amincewar muhalli ba.
Ta ƙara da cewa sare itatuwa ba bisa ka’ida ba laifi ne, yana cutar da muhalli kuma cin amanar ƙasa ne, kuma hakan na iya janyo tara mai tsanani ko ɗaurin kurkuku bisa dokokin da ake da su.
Kwamishinan ya buƙaci al’umma da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta da izini, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnatin jihar na ci gaba da jajircewa wajen kawar biranen Kano yayin da take aiwatar da muhimman ayyukan more rayuwa cikin mutunta muhalli.













































