Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirin kafa dokar ‘yancin samun bayanai a matakin jiha, domin ƙarfafa ‘yancin ‘yan jarida da kuma bai wa al’umma damar samun bayanan gwamnati yadda ya kamata.
Wannan shiri na nuni da sabon ƙuduri na gwamnati wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da buɗaɗɗen mulki a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Ciki na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya gabatar da wannan batu yayin wani taron horaswa na kwanaki biyu da aka shirya wa mambobin ƙungiyar Kano Online Media Chapel a Jihar Jigawa.
Taron ya mayar da hankali kan inganta ƙwarewa da ɗabi’ar aikin jarida a kafafen internet.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ƙungiyar Kano Online Media Chapel ce ta shirya taron tare da goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano, inda taken taron ya ta’allaka ne kan ingantacciyar ɗabi’a da mu’amala mai kyau a aikin jarida ta internet.
Dokar da ake shirin kafawa za ta yi kama da dokar ‘yancin samun bayanai ta ƙasa, wadda ke kare ‘yancin faɗar albarkacin baki da samun bayanai.
Gwamnatin ta nuna aniyar ci gaba da kare haƙƙin ‘yan jarida, tare da jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin sana’a da ɗabi’a, musamman a Kano wadda ke da yalwar jama’a da kuma yanayin siyasa mai sarkakiya.
Karanta: Kwankwaso ya lissafo sharaɗi kafin komawa APC
Ya bayyana cewa aikin jarida ta internet ya zama muhimmin ginshiƙi a aikin jarida na zamani, wanda ke buƙatar ƙwarewa, gaskiya da ci gaba da koyon sabbin dabaru, musamman a wannan zamani da fasahar kere-kere da basirar AI ke tasiri sosai, inda ya ƙarfafa ‘yan jarida su gina sunansu bisa gaskiya da daidaito domin samun amincewa a sana’ar.
Tun da fari, shugaban Kano Online Media Chapel, Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin cika alkawarin da aka ɗauka lokacin ƙaddamar da ƙungiyar na fifita horaswa ga mambobinta.
Ya ƙara da cewa irin saurin aikin jarida ta internet na buƙatar sanin dokoki da ɗabi’u domin kauce wa yaɗa bayanan ƙarya ko tayar da rikici.
Haka kuma, shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta Jihar Kano na kungiyar ‘yan jarida ta ƙasa NUJ, Suleiman Abdullahi Dederi, ya yaba da rawar da Ma’aikatar Yada Labarai ta taka wajen shirya taron, yana mai bayyana cewa hakan na da matuƙar muhimmanci wajen kare makomar aikin jarida a jihar.
Shugaban NUJ na Jihar Jigawa, Ismaila Ibrahim, ya nuna cewa kafa ƙungiyar Online Media Chapel a jihar zai ƙarfafa haɗin kai da musayar ilimi tsakanin ‘yan jarida na jihohi.












































