Gwamnatin jihar Yobe ta umarci a rufe dukkanin makarantun sakandaren kwana saboda tsaro

Mai Mala Buni 685x430

Gwamnatin jihar Yobe ta bada umarnin rufe dukkanin makarantun sakandaren kwana a faɗin jihar domin kare ɗalibai daga barazanar tsaro da ke ta ƙaruwa a wasu yankuna na ƙasar.

Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Harkokin Jama’a na gwamna Mai Mala Buni, Alhaji Mamman Mohammed, ya fitar a Damaturu ranar Asabar.

Sanarwar ta ce an yanke wannan shawara ne bayan wani taron tsaro da gwamnan ya jagoranta tare da shugabannin hukumomin tsaro na jihar, inda aka tattauna rahotannin matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu makarantun jihohin ƙasar.

Mohammed ya ce matakin ya zama dole bayan duba yadda wasu hare-hare da rashin tsaro suka jawo barazana ga tsaron makarantun a wasu jihohi, lamarin da ya tilasta ɗaukar mataki kafin abin ya shafi jihar Yobe.

Karanta: Sojoji sun kama wani da ake zargi da laifin yin garkuwa, daidai lokacin da yake tattaunawa kan Naira Miliyan 20 a matsayin kuɗin Fansa

Ya bayyana cewa Gwamna Buni ya yi kira ga jama’a da su yi addu’a ga shugabanni, jami’an tsaro, don samun zaman lafiya da kyautatuwar tsaro a jihar da ƙasar baki ɗaya.

Sanarwar ta bayyana cewa Babban sakataren Ma’aikatar Ilimi Dakta Bukar Aji-Bukar, ya tabbatar da cewa rufe makarantun na ɗan lokaci ne, har sai an sami kwanciyar hankali a yanayin tsaro.

Sanarwar ta umarci dukkan shugabannin makarantun da abin ya shafa da su tabbatar da cikakken bin wannan umarni.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here