Gwamnan Kano ya gargadi kwamishinoni kan fitar da sirrikan gwamnati

WhatsApp Image 2026 01 17 at 01.27.38 750x430

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi mambobin majalisar zartarwa ta jihar kan ayyukan rashin biyayya da kuma fitar da bayanan gwamnati.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa gwamnan ya yi wannan gargadi ne yayin taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 38 da ke gudana a gidan gwamnati da ke Kano a ranar Alhamis.

A yayin taron, gwamna Yusuf ya bayyana cewa wasu kwamishinoni sun riga sun ajiye mukamansu sakamakon sabbin daidaituwar siyasa da suka faru a jihar.

Ya sanar da cewa daga cikin jimillar kwamishinonin, biyar sun ajiye mukamansu kuma ya amince da murabus din nasu, tare da yi musu fatan alheri a abubuwan da za su yi a gaba.

Gwamnan ya kuma bukaci sauran mambobin majalisar zartarwar su sake jaddada biyayyarsu ga wannan gwamnati da kuma manufofin jam’iyyarsu ta siyasa.

Ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin mambobin gwamnati, yana mai cewa ana bukatar kokarin hadin gwiwa domin cika alkawuran da gwamnatin ta dauka ga al’ummar jihar.

Gwamna Yusuf ya kuma gargadi cewa dole ne a kawo karshen rabuwar kai a cikin gwamnati, rashin biyayya da kuma fitar da bayanai daga cikin gwamnati.

Ya bukaci mambobin majalisar su mayar da hankali kan ayyukansu tare da nuna jajircewa wajen gudanar da nauyin da aka dora musu, yana mai gargadin cewa duk wanda ya saba da ka’idoji da manufofin wannan gwamnati za a cire shi daga mukaminsa.

A halin da ake ciki kuma, mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, bai halarci taron ba.

Rahotanni sun nuna cewa Gwarzo bai amince da komawa APC tare da gwamnan ba, kuma bai ajiye mukaminsa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here