Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyarsa ta (NNPP), ya na mai danganta matakin da tsanantar rikice-rikicen cikin gida da kuma bukatar kare muradun al’ummar Kano.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, gwamnan ya aike da wasiƙar murabus ɗinsa zuwa ga shugaban NNPP na mazabar Diso-Chiranchi da ke ƙaramar hukumar Gwale, inda ya bayyana cewa ficewar za ta fara aiki daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.
A cikin wasiƙar, Gwamna Yusuf ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi tun daga shekarar 2022, tare da gode wa shugabanni da mambobin NNPP a Kano bisa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi a tsawon lokacin da yake jam’iyyar.
Sai dai ya bayyana cewa rikice-rikicen shugabanci da shari’o’in da ke gudana a kotuna sun raunana tsarin jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. Ya ce waɗannan matsaloli sun haifar da rabuwar kai da rashin jituwa mai tsanani a tsakanin ƴaƴan jam’iyyar.
Gwamnan ya ce bayan dogon tunani, ya yanke shawarar ficewa daga NNPP ne bisa la’akari da muradin jama’a, yana mai jaddada cewa matakin da ya ɗauka ba tare da wata ƙiyayya ko ɗacin rai ba, sai don tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya fice daga jam’iyyar ne tare da ‘yan majalisar dokokin jiha 21, ‘yan Majalisar Wakilai 8 da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.
Jam’iyyar NNPP a mazabar Diso-Chiranchi ta tabbatar da karɓar wasiƙar murabus ɗin, inda sakatarenta, Hon. Kabiru Zubairu, ya yaba wa gwamnan bisa ayyukan raya kasa da ya aiwatar a fannoni daban-daban.












































