Goodluck Jonathan yana cikin ƙoshin lafiya, kuma ya bar Guinea-Bissau – Gwamnatin Tarayya

Jonathan waving

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan yana cikin koshin lafiya kuma ya bar Guinea-Bissau bayan sabbin lamuran siyasa da suka faru a ƙasar ta Afirka Yamma.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ne ya bayyana haka ga ‘yan jarida a Abuja ranar Alhamis.

Ebienfa ya tabbatar cewa Jonathan ya bar Guinea-Bissau tare da sauran mambobin tawagarsa a jirgin sama na musamman.

A cewarsa, tsohon shugaban ƙasa ya tashi tare da mambobin tawagarsa, ciki har da babban ɗan diflomasiyya Ibn Chambas.

Labari mai alaƙa: Juyin mulki a Guinea-Bissau: Majalisar wakilai ta buƙaci gwamnatin tarayya ta tabbatar tsohon shugaban ƙasa Jonathan ya dawo Lafiya

Jonathan ya kasance a Guinea-Bissau a matsayin wani ɓangare na aikin ƙasa da ƙasa kafin lamarin juyin mulki ya tilasta masa barin ƙasar da wuri.

Tsohon shugaban ƙasa ya tafi Bissau a matsayin ɓangare na tawagar ƙasa da ƙasa don lura da zaɓen ƙasar, amma ya makale a ƙasar bayan sojoji su ka kwace mulki kuma su ka rufe duk hanyoyin sufuri.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here